Makamai: Ba mu aikata laifi ba —Nigeria

Kanar Sambo Dasuki mai ritaya Hakkin mallakar hoto The Will
Image caption Hukumomin tsaro a Nigeria sun ce babu wani bakon abu a matakin da suka dauka

Ofishin mai baiwa shugaban Najeriya shawara a kan al'amuran tsaro ya ce kudin da aka bayar da rahoton kamawa a Afirka ta Kudu, inda aka je sayen makamai, kudi ne na halal.

Ofishin na mai da martani ne ga rahotannin da aka bayar na kwace dalar Amurka miliyan biyar da dubu dari bakwai wanda aka tura daga Najeriya da nufin sayo makamai.

A wata sanarwa da ya fitar, ofishin mai ba da shawarar, Kanar Sambo Dasuki mai ritaya, ya ce kudin da ake magana ba haramtaccen ciniki ake je yi da su ba.

Sanarwar mai dauke da sa hannun kakakin Kanar Duskin, Karounwi Adekunle, ta ce hakika "an kulla hulda ta cinikayya tsakanin wani halaltaccen kamfani na Najeriya da wani halaltaccen kamfanin na Afirka ta Kudu, kuma an bayar da kudi ta hanyar banki".

Sai dai kuma a cewar Mr Adekunle, daga bisani kamfanin na Afirka ta Kudu ya ga cewa ba zai iya samar da hajojin da aka yi da shi zai samar ba, don haka ya yanke shawarar maido da kudin.

Jiya Litinin ne dai wasu kafofin yada labarai na Afirka ta Kudu suka ba da rahoton cewa hukumomin kasar sun sake kwace wasu kudi da aka shiga da su kasar don sayen makamai.

A cewar jaridar City Express ta Afrika ta Kudun, a da kamfanin na Afirka ta na da lasisin cinikin makamai daga hukumar da ke sa ido a kan kananan makamai ta Afirka ta Kudun, amma a watan Mayun bana lasisin ya daina aiki.

A watan na Mayu kuma izinin yin wannan ciniki ya daina aiki shi ma, al'amarin da ya sa kamfanin na Afirka ta Kudu ya yanke shawarar mai da kudin.

Kwace wannan kudi na zuwa ne kasa da wata guda tun bayan da hukumomin kasar ta Afirka ta Kudu suka kame wadansu 'yan Najeriya biyu da wani dan Isra'ila da tsabar kudi dalar Amurka miliyan tara da dubu dari uku.

Hukumomin Afirka ta Kudu dai sun nuna shakku a kan wadancan kudi, wadanda aka shiga da su kasar a wani jirgin sama mallakar shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya, Pastor Ayo Oritsejiafor, suna masu cewa kamfanin da aka kulla cinikin da shi bai da hurumin sayar da makamai a kasar.

Wasu majiyoyin hukumomin tsaro a Najeriya sun ce labaran kafofin yada labaran Afirka ta Kudun na ranar Litinin sun tabbatar da cewa wancan cinikin ma an yi shi bisa ka'ida, saboda akwai takardun dake nuna cewa an samu amincewar mai baiwa shugaban kasar Najeriya shawara a kan lamuran tsaro kuma hukumomin Afirka ta Kudun na da masaniya.

Karin bayani