Twitter ya kai gwamnati Amurka kotu

Shafin sada zumunta na Twitter ya shigar da kara gaban kotu inda ya ke tuhumar gwamnatin Amurka da sabawa dokokin sa ido.

Karkashin dokokin na yanzu, Twitter ba zai iya bayana wasu bayanai a kan tsaro da gwamnati ke bukata kan masu amfani da shafin ba .

Kamfanin ya ce matakin ya sabawa yancin tofa albarkacin baki kamar yadda kundin tsarin mulkin Amurka ya tanada.

Hakkin mallakar hoto AFP

Twitter ya ce ya shigar da karar ne a matsayin wani yunkuri domin tilastawa gwamnatin Amurka wajen ganin ta dinga kwatantata adalci a kan bukatunta na samar mata da bayanai mutane.

" Mun yi ammanar cewa kundin tsarin mulkin ya ba mu damar maida martani kan damuwar da masu amfani da shafin suka nuna da kuma furucin da jamian gwamnatin Amurka ke yi na samar masu da bayanai domin su rika sa ido akan abubuwan da ke wukana". LauyanTwitter , Ben Lee ya rubuta a cikin shafinsa.

Ranar talatar da ta gabata ne kamfanin ya shigar da kara gaban kotu a California inda ya ke tuhumar ma'aikatar sharia da kuma hukumar bincike ta FBI .

Hakkin mallakar hoto Getty

A watan avrilun daya gabata ne kamfanin ya gabatar da wani rahoto ga gwamnatin Amurka domin ta wallafa sai dai kawo yanzu jamian kasar sun ki amincewa da bukatar Twitter na gabatarwa jama'a da rahoton baki dayansa.

Rahoton ya kunshi bayanai akan kaidojjin kamfanin dangane da bayanai da suka shafi tsaron cikin gida.

Sai dai duk da cewa yawan bukatun da Twiter ke samu daga wurin gwamnati be kai na Google ba , sai dai wata kungiyar farar hula da da ake kira American Civil Liberties Union ta ce watakila matakin ya sa sauran kamfanonin shafukan internet su dauki mataki.