Gwamnan Adamawa: An yanka ta tashi

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kotun wadda ke zamanta a Abuja ta ce Ahmed Fintiri ba halartaccen Gwamnan riko ba ne.

Wata babbar kotun tarayya a Nigeria ta yanke hukuncin cewa rantsar da Ahmed Fintiri a matsayin gwamnan jihar Adamawa na riko haramtacce ne, kuma ya saba wa tsarin mulkin kasar.

Don haka ta umarci Cif Jojin jihar Adamawa ya gaggauta rantsar da tsohon mataimakin Gwamna Murtala Nyako, Bala Ngilari, a matsayin gwamnan jihar.

Alkalin kotun mai shari'a Adeniyi Ademola ya bukaci Umaru Fintiri ya sauka daga mukamin gwamnan jihar nan take, sannan a rantsar da Barrister Bala Ngilari a matsayin gwamna ba tare da wani bata lokaci ba.

Mai shari'a Adeniyi ya ce rantsar da Umaru Fintiri a matsayin mukaddashin gwamnan jihar, haramtacce ne don haka ya sabawa doka.

Mr. Bala Ngilari shi ne mataimakin tsohon gwamnan jihar Murtala Nyako wanda aka tsige daga mukaminsa na gwamna a ranar 15 ga watan Yuli sakamakon rashin iya gudanar da mulki.

Bala Ngalari ya mika takardar barin kujerar mataimakin gwamna ga kakakin majalisar dokokin jihar, Umaru Fintiri, amma ya garzaya kotu daga baya, inda ya bukaci a rantsar da shi kan mukamin gwamna saboda a cewarsa doka ta tanadi cewa ya mika takardar barin aiki ga gwamna ne amma ba kakakin majalisar ba.

Hukumar zabe mai zaman kanta a Nigeria ta shirya gudanar da zaben cike gurbin kujerar gwamnan jihar ta Adamawa a ranar Asabar 11 ga watan Oktoba, amma kotun karkashin mai shari'a, Ademola ta dakatar da hukumar inda ta ce Ngilari bai ajiye aiki ba, kafin tsige gwamna Murtala Nyako.