An rantsar da Ngilari, gwamnan Adamawa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ministan shari'ar kasar ya bukaci alkalin alakalan jihar Adamawa ya rantsar da Ngilari a kan mukamin gwamna

Rahotanni daga jihar Adamawa a arewa maso gabashin Nigeria na cewa an rantsar da mataimakin gwamnan Jihar, Barista Bala James Nigilari, a matsayin sabon gwamnan jihar.

Matakin ya biyo bayan hukuncin da wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yanke ne cewa alkalin alkalan jihar ya rantsar da tsohon mataimakin gwamnan a mukamin gwamna, saboda murabus din da aka ce ya yi, ba ya bisa doka.

Yayin rantsar da shi, Barista Bala James Ngilari, ya yi alkawarin aiki bisa tanade-tanaden dokokin kasar.

Tsohon mukaddashin gwamnan jihar, Alhaji Ahmadu Umaru Fintri, wanda hukuncin kotun ya umarce shi ya sauka daga mukamin, ya bayyana cewa ya daukaka kara kan wannan hukunci.

Hukumar zabe ta kasa INEC ta bayyana cewa za ta yi aiki da hukuncin kotun na dakatar da sabon zaben cike gurbi da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar mai zuwa.