Ko biri na da 'yanci daidai da na mutum?

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata kotu a bara ta haramta irin wannan 'yanci da zai ba da damar sauya wa birin matsugunni

Wata kotun daukaka kara a New York din Amurka na sauraron wata shari'ah a Larabar nan, kan ko gwaggon biri na da 'yanci daidai da na dan'Adam ta fuskar shari'ah.

Wata kungiyar kare hakkin dabbobi, Nonhuman Rights Project ce ta shigar da karar, inda ta bukaci kotu ta yi hukunci kan matsayin wani gwaggon biri da ake kira Tommy, wanda aka ajiye shi a wani karamin keji cikin duhu a jihar New York.

Kungiyar ta ce gwaggon birrai na da hakkin abin da ta kira 'yancin watayawa.

Wannan shari'a, ita ce irinta ta farko, kuma idan kungiyar ta yi nasara, za ta bude kofar shari'o'i a madadin wasu dabbobi.