'Wasu ma'aikatan lafiya za su kamu da Ebola nan gaba'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Cutar Ebola ta kashe mutane fiye da 3000 a yammacin Afirka

Babban masanin Kimiyyar nan kuma mashawarcin hukumar Lafiya ta Duniya akan cutar Ebola, ya ce bai yi mamaki ba, ganin cewa wata ma'aikaciyar jinya 'yar Spaniya ta kamu da cutar a wani asibiti dake Madrid, a lokacin da take kula da wasu masu dauke da cutar su biyu wadanda kuma suka mutu daga baya.

Farfesa Peter Piot, wanda shike shugabantar kwamitin Kimiyya na hukumar lafiyar ta duniya, ya ce duk irin kankantar kuskuren da aka samu a lokacin da ake kula da mara lafiyar dake dauke da kwayar cutar, ka iya kasancewa wani al'amari mai hatsari.

Ya ce yana kuma tsammanin za 'a samu karin ma'aikatan lafiyar da zasu kamu da cutar, koma a kasashen da suka cigaba, wadanda kuma suke da tsarin kiwon lafiya na zamani.

Cutar Ebola ta kashe fiye da mutane 3000 a yammacin Afirka