Facebook da Twitter da Google zasu halarci taron yaki da ta'addanci

Hakkin mallakar hoto Reuters

Za a gudanar da wani liyafar cin abincin dare tsakanin kamfanonin fasahar da kuma jami'an gwamnati daga daukacin kasashen turai a ranar Laraba

Manufar taron shine a tattauna hanyoyin dakile harkar masu tsattsauran ra'ayi a Internet da kuma hadin kai tsakanin kungiyar EU da kuma wasu mahimman shafukan internet

Twitter da Google da Microsoft da kuma Facebook za su halarci Taron

Gwamnati na kara nuna damuwa game da yadda masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama ke amfani da shafukan sada zumunta wajen daukar mambobinsu.

Kungiyar Tarayyar Turai wato EU za ta yi karin bayani game da taron a ranar Laraba gabanin liyafar cin abincin daren da za'a yi.

Ministoci daga kasashe 28 mambobin EU, da kuma mambobin hukumar tarayyar turai da kuma wakilai daga kamfanonin fasaha ne zasu halarci Taron.

Hukumar Tarayyar Turai ta ce: 'Kungiyar Tarayyar Turai da kuma ministocin cikin gida na da matukar sha'awar yin wata tattaunawa tare da manyan kamfanonin Internet akan batutuwan da suka shafi amfani da Internet wajen yada tsatsauran ra'ayi.

Hakkin mallakar hoto Getty

BBC ta fahimci cewa wannan shi ne karo na biyu tun watan Yuli da aka gayyaci kamfanoni domin tattauna wadannan matakai na hana amfani da shafukan internet kamar su Twitter da Facebook wajen yadawa da kuma yadda ana amfani da su wajen daukar masu tsatsauran ra'ayin addinin Islama.

Sai dai wani kamfani da aka lura da cewa baya cikin taron shi ne Ask.fm, wanda aka yi imanin cewa kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama na amfani da shi matuka.

IIja da kuma Mark Terebin sune masu kamfanin, amma sai dai wani kamfanin Amurka ya saye shi daga baya

Wadanda suke mallakar sa sun shaidawa BBC cewa: 'Ba a gayyaci Ask.fm zuwa wajen tattaunawar ba'

'Idan da mun san da taron, da mun je, tabbas'

Ministan tsaro na gwamnatin Burtaniya James Brokenshire ne zai wakilci kasar a taron.

Ya fadawa BBC cewa ' ba mu yarda da kasancewar 'yan ta'addar Internet ba, da kuma farfagandar masu tsatsauran ra'ayi

Kiyasi a yanzu ya nuna cewa yawan 'yan Burtaniya da aka dauke su, domin yaki ga kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi a Syria da Iraqi sun fi mutane 500