'Dole a dauki mataki a kan Kobane'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Garin Kobane ya na Syria

Wakilin Majalisar dinkin duniya na musamman ga Syria ya ce dole ne Kasashen duniya su yi duk irin abinda zasu iya, wajen kare fadawar garin Kobane karkashin ikon mayakan Islama

Staffan di Mistura ya fadawa BBC cewa rasa garin Kobane ga mayakan, ka iya kasancewa wata babbar barazana ga makwabciyar kasar Turkiyya

Ya ce 'duniya da dukkaninmu zamu yi nadama sosai, idan har mayakan ISIS suka kwace Kobane wanda ya kare kansa da karfin hali, a yanzu ana bukatar daukar mataki'

Wani Komandan Kurdawa a garin Kobanen, ya fadawa BBC cewa hare- hare da sojoji suke kaiwa yana yin tasiri matuka, amma fa ya ce ana bukatar karin hadin- kai tare da mayakan kurdawa dake kasa