Nijar ta yi jana'izar wasu sojojinta 9

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu shugabannin kasashen duniya sun aika da sakon ta'aziyyarsu game da mutuwar sojojin

An yi jana'izar sojojin jumhuriyar Nijer tara da aka kashe yayin aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Mali.

An karrama sojojin wadanda ke aiki a rundunar wanzar da zaman Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali Minusma, ta hanyar yi musu jana'izar ban girma.

Kafin gudanar da jana'izar, sai da ma'aikatar tsaron kasar ta karrama sojojin a harabar dakin ajiye gawawwaki na babban asibitin Niamey, inda ministan tsaro na kasar Mali da wakilin majalisar dinkin duniya a yankin afrika ta yamma suka hallara.

An kashe sojojin ne a wani kwanton bauna da wasu masu dauke da makamai suka yi musu a kasar Mali.