Amurka na son amfani sansanin sojin saman Turkiyya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Turkiyya na son a kirkiri wani yanki na tudun mun tsira amma Amurka bata so

Amurka tace samun damar shiga sansanin sojin sama na Incirlik a Turkiyya, shine irin taimakon da take fatan ganin ta samu daga Ankara, a Yakin da take yi da mayakan Islama.

Sakataren Tsaro Chuck Hagel ya kuma ambato taimako na horo da kuma baiwa dakarun 'yan adawar Syria makamai.

Ya ce 'za'a tayarda wadannan batutuwa a tattaunawar da za'a yi da Shugabannin Turkiyyan a wannan makon'.

A waje guda kuma, Amurkawan na cigaba da kai hare- haren sama akan mayakan Islamar dake luguden wuta a Kobane.

Wata kungiyar dake sa-ido a London tace kungiyar IS ta kwace ikon fiye da kashi uku na garin Kobanen. Sai dai kurdawa sun musanta wannan ikirari