An far wa 'yan gudun hijira a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu shaidu sun ce maharan sun fara auka wa jami'an tsaron Kamaru ne kafin su koma kan 'yan gudun hijira

Wasu mutane dauke da makamai sun auka wa wasu 'yan gudun hijiran jihar Borno da ke garin Kerawa Mafa na jamhuriyar Kamaru, da tsakar dare.

Rahotanni sun ce maharan sun shiga Kamaru ne daga kan iyakar Nigeria dauke da manyan makamai, inda suka far wa mutane a gidaje da sauran wuraren da aka tsugunnar da su.

Maharan sun kashe mutane da dama a lokacin da 'yan gudun hijirar ke kwance, kuma sun rusa wasu gidaje.

'Yan gudun hijirar da ke tsere wa rikicin Boko Haram sun ce sun rasa hanyar da za su binne gawawwakin mutanen da aka kashe don kuwa har zuwa wayaewar gari suna jin amon bindigogi.