Ebola: An killace ma'aikaciyar jinya a Australia

Hakkin mallakar hoto
Image caption A ranar Laraba wani dan Liberiya ya mutu a Amurka

An killace Wata ma'aikaciyar Jinya 'yar Kasar Australia a wani asibiti dake arewacin garin Cairns saboda fargabar maiyiwuwa ta harbu da kwayar cutar Ebola yayinda take aiki a Saliyo.

Bayan komawar Ma'aikaciyar Jinyar gida ne a karshen mako, ta kama zazzabi,

Ana dai saran samun sakamakon gwaje- gwajen da aka yi mata a 'yan sa'oi masu zuwa.

An ruwaito cewa ta fadawa Likitoci cewa ta sanya rigar kariya a dukkanin lokutan da tai aiki a Saliyo, kuma bata saba duk wata ka'ida ba

Wannan shine na'uin cutar na baya- bayan nan a wajen yankin Afirka

Yanzu haka ma dai ana yiwa wata ma'aikaciyar jinyar magani a Spain saboda cutar da kuma wasu karin ma'aikatan lafiya uku