Ebola: Shugabanni sun yi taron koli

Ebola Hakkin mallakar hoto Reuters

Shugabannin kasashen Liberia, Saliyo da kuma Guinea, wadanda cutar Ebola ta fi kamari sun mika kokon bararsu na neman taimako don yakar wannan cuta ta Ebola.

A wani taron Babban Bankin Duniya da aka gudanar a Amirka, Shugaban Saliyo, Ernest Bai Koroma, ta bayyana cewa duniya ta nuna halin ko-in-kula ganin yadda yara ke zama marayu ga kuma likitoci da ma'aikatan jiyya na rasa rayukansu.

Ya ce, "Al'umarmu sai mutuwa suke, yara na zama marayu.

Wadanda ke mutuwa mafi yawansu mata ne, kuma fiye da kashi biyu cikin uku da ke da cutar masu matsakaitan shekaru ne."

Mataimakin shugaban hukumar lafiya ta duniya, Bruce Aylward, ya fada wa taron cewa Ebola ta warwatsu cikin biranen kasashen uku tana kuma kara ci gaba da shiga wasu bangarorin.

Wani babban jami'in kula da lafiya na Amirka, Thomas Frieden, ya ce barkewar cutar Ebola ta sha babban da kowace irin cuta tun bayan cuta mai karya garkuwar jiki watau HIV.