Wasu 'yan Nigeria sun kai shugaban CAN kotu

Shugaban kungiyar kiristoci a Najeriya
Image caption Shugaban kungiyar kiristoci a Najeriya

Wasu 'yan Nigeria da suka hada da malaman jami'a sun nemi kotu ta tilastawa shugaba Goodluck Jonathan da shugaban kungiyar kiristoci ta kasar watau CAN da suyi cikakken bayani mai gamasarwa, kan batun kudin nan na makamai da hukumomin Afrika ta kudu suka kama.

Haka kuma mutanen sun nemi kotun ta tilastawa Majalisar dokokin kasar da wasu hukumomi su gudanar da bincike kan batun, sannan su fito da sakamakon binciken ga jama'a.

Su dai hukumomin Nigeria na cewa an gudanar da cinikin ne ta halattaciyar hanya.

Amma mutanen da suka shigar da karar sun ce sam basu gamsu ba, domin akwai alamomin tambaya kan hanyoyin da aka bi, wajen sayo makaman.