Ana kukan karancin wuta a Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nijar na fuskantar karancin wuta

A jamhuriyar Nijar wasu kungiyoyin kare hakkin jama'a sun koka a kan matsalar karancin wutar lantarkin da kasar ke fuskanta

Kungiyoyin sun ce lamarin na yin matukar tasiri ga kokarin da 'yan kasar ke yi, na habbaka tattalin arziki da kyautata jin dadin rayuwar al'umar kasar .

Amma sai dai ma'aikatar ministan makamashi da man fetur ta ce gwamnati na iyakacin kokarinta domin wadata kasar da wutar lantarkin.

Ma'aikatar ta kuma ce karancin ma'aikatan da zasu rinka auna yawan wutar da jama'a suke amfani da ita na daga cikin dalilan da suke janyo matsala a harkar samar da wuta.