Ana share bayanan cikin waya daga nesa

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Babu cikakken bayani game da yadda ake share abubuwan cikin waya tun daga nesa

BBC ta fahimci cewa ana share dukkanin bayanan dake cikin wayoyin da aka kwace domin samun shaida tun daga nesa , a lokacin da suke a hannun 'yan sanda

'Yan sanda a Cambridgeshire da na Derbyshire da na Nottingham da Durham sun fadawa BBC cewa an share bayanan cikin wayoyin da suka kwace tun daga nesa

Kuma 'yan sandan Dorset sun ce wannan al'amari ya auku ga wasu wayoyi guda shida da suka kwace, wadanda kuma ke hannunsu a cikin shekara guda

An kirkiri wannan Fasahar domin baiwa masu mallakar wayoyi damar share duk wani abu dake cikin wayoyinsu tun daga nesa idan an sace wayoyin

Wata mai magana da yawun 'yan sandan Dorset ta fadawa BBC cewa 'sau shida haka ta faru kuma bamu san yadda mutane suke share bayanan cikin wayoyinsu ba dake hannunmu'

Ita ma mai magana da yawun 'yan sandan Derbyshire ta tabbatar da cewa rundunarsu ta taba ganin irin wannan lamari, inda aka share bayanan wata waya dake hannunsu

A waje daya kuma 'yan sandan Cleveland sun fadawa BBC cewa su ma sun taba ganin irin wannan lamari na wata waya da aka share abubuwan dake cikinta amma basu tabbatar ba ko an share abubuwan cikin nata ne kafin ta zo hannunsu