Ebola ta kara kamari a yammacin Afrika

Wata mata da ake yi wa gwaji Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wata mata da ake yi wa gwaji

Hukumar lafiya ta duniya ta yi gargadin cewa yanayin da ake ciki a kasashe uku da cutar ebola ta fi kamari ya yi kara muni a cikin kwanaki goma sha biyu da suka wuce.

Mataimakin shugaban hukumar Bruce Aylward ya ce kusan kashi sabain cikin dari na wadanda suka kamu da cutar a manyan biranen Liberia da Guinea da kuma saliyo na mutuwa kuma cutar na yaduwa fiye da yadda ake tsammani.

Ita ma kungiyar liktoci ta ce dole ne duniya ta dauki mataki nan take, domin kare aukuwar wani babban bala'i.

Shugabar Kungiyar Likitoci ta Medecins Sans Frontieres, ta ce ta kasa fahimtar mai-yasa za a ce watanni bakwai bayan barkewar cutar Ebolar, har yanzu ba a kaiga jibge dimbin ma'aikatan da zasu kai -dauki a yankin Afirka ta Yamma ba

Shi ma Shugaba Alpha Conde na Gini inda cutar ta soma barkewa, yace da- a ce duniya ta maida hankali da gaske, da tuni an shawo kan cutar.