An kwace kadarorin wani mataimakin Shugaban Kasa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cin hanci da rashawa na daga cikin matsalolin dake addabar Kasashen Afirka

An tilastawa wani mataimakin Shugaban Kasa na Equatorial Guinea mika wasu kadarorinsa na dala miliyan Talatin da ya mallaka a Amurka, wanda hukumomi suka ce an mallake sune da kudaden sata.

Dole ne kuma Teodoro Ngume Obiang- ya saida wasu abubuwa da ya mallaka , ciki harda katafaren gidansa dake Malibu da kuma wata motarsa ta hawa kirar Ferarri da kuma wasu mutum- mutumi guda shida na fitaccen mawakin nan Michael Jackson.

Ma'aikatar shari'ah ta Amurka tace wannan al'amari ya nuna cewa kasar ba waje bane da ake tara kudaden da aka samu ta hanya mara kyau.

Mr Obiang dai ya ce ya sayi kadarorin ne da kudaden da ya samu ta halartacciyar hanya