Guinea: Jirgin ruwa ya kife da jama'a

Hakkin mallakar hoto f
Image caption Mutane da dama ne ke cikin jirgin

Mutane 9 ne suka mutu sannan da dama ba'a gansu ba, bayan wani jirgin ruwa ya kife cikin kogi a kasar Guinea.

Rahotanni sun ce hatsarin ya auku ne da yammacin ranar juma'a, a kudu maso gabashin Kasar, kusa da iyakar kasar da Saliyo.

Jami'ai sun ce an ceto 18 daga cikin mutane 69 dake cikin jirgin kafin faduwar rana