Boko Haram sun sako mutane 27 a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP

'Yan Kungiyar Boko Haram sun sako wasu mutane 27 da suka sace a Jamhuriyar Kamaru.

Cikin wadanda aka sakon harda matar mataimakin fira-ministan kasar Ahmadou Ali wadda aka sace a watan Yuli da kuma wasu 'yan China goma da aka sace a watan Mayu, a kusa da iyakar kasar da Najeriya.

Ministan sadarwar kasar, Issa Tchiroma Bakary, ya ce Shugaba Paul Biya ne da kansa ya taka rawa wajen sako wasu mutanen.

A hirarsa da BBC, ministan ya ce sakon mutanen wata babbar nasara ce.

Babu tabbacin ko an biya kudin fansa kafin a sako mutanen.

Kungiyar Boko Haram ta fadada hare-harenta a 'yan kwanakin nan zuwa wasu yankunan arewacin Kamarun.

Rahotanni sun nuna cewa tuni har an dauki mutanen a jrgin sama zuwa Yaounde, babban birnin kasar, kuma jama'a na murna hakan.

Alhaji Shu'aibu Garkuwa, Garkuwan Ngoundere, da ke arewacin kasar, ya gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa jama'ar Kamaru na farin ciki sosai akan sako mutanen.

Karin bayani