Ebola: 'A kafa asusun duniya'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mr Jim Y0ong Kim ya kuma nemi da a yi wani shiri don tunkarar wata annobar da ka iya fin Ebola a gaba

Shugaban bankin duniya Mr Jim Yong Kimya yi kiran ne da a samar da asusu na musamman da za a yi amfani da shi wajen tunkarar manyan-manyan kalubalen matsaloliln lafiya da suka addabi duniya, musamman cutar Ebola.

Mr Jim Yong Kim yayi rokon ne a wurin taron shekara-shekara na bankin na duniya a Washington.

Rokon dai ya biyo bayan sukan da ake yi ne cewa kasashen duniya ba sa daukar matakan da suka dace na yaki da annobar ta Ebola.

Shugaban bankin na duniya ya ce kudin da za a samar a asusun za a rika taimaka wa kasashen da suka samu kansu cikin duk wata matsala ne ta cuta.

Kiran nasa dai maimaici ne na abin da kasashen Yammacin Afrika uku da cutar ta Ebola ta fi yi wa banna, wato Liberia da Saliyo da kuma Guinea, da suke kokawa cewa matakan da kasashen duniya ke dauka na dakile cutar sun yi kadan matuka.

Karin bayani