Na'urar cajin kudin dariya

Masu shire-shiren ban dariya Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu shire-shiren ban dariya

Wani Kulob na masu shire-shiren ban-dariya a Bercelona yana gwajin wani tsari na cajin 'yan kallo kudi kwatankwacin dariyar da suka yi, ta hanyar makala wata na'ura da za ta yi nazarin fuskokinsu don yanke shawarar kudin da za a caje su idan sun ji dadin ba su dariyar da aka yi.

Na'urar da za ta rinka wannan nazari an makala ta ne a kan teburan dake like da kujerun da aka kakkafa a Kulob din Teatreneu.

Kowacce dariya dan kallo ya yi za a caje shi kudi euro santi 30.

An bullo da wannan tsari ne don kawo karshen raguwar da ake samu ta masu zuwa gidajen shire-shiren ban-dariyar.

Tare da hada hannu da Kulub din ya yi da wani kamfani na tallace-tallace da ake kira Cyranos McCann, gwajin tamkar martani ne ga karin da gwamnati ta yi na haraji kan tikitin shiga gidajen kallon, dalilin da ya tilasta ma wasu kaurace ma gidajen kallon.

Akwai alamun wannan gwaji da ake yi ya yi tasiri saboda a cewar gidajen kallon farashin tikitin ya karu da euro 6.

A yanzu haka dai sauran gidajen kallo a kasar Spaniya suna cigaba da kwaikwayon wannan tsari.

Haka nan kuma Club din na masu shire-shiren ban-dariyar ya bullo da wani tsari na biyan kudin shiga ta wayar salula da kuma wani tikitin mai sauki na shirin ban-dariya na farko.

James Woroniecki darakta na London 99 Club, ya ce, "wannan abu ne mai kyau, muddin dai ba a mika bayanan fuskokin mutanen ba ga hukumar tsaro ta Amurka.

Yace, "zai zamo babban kalubale na fasaha - kamar yadda mutane ke dariya a kulub din 99, lallai ne mu sanya na'urar nan a kowacce kujera.

Karin bayani