An sace tsohon shugaban lauyoyin Najeriya

Hakkin mallakar hoto AFP

A Najeriya rundunar 'yan sanda a Jihar Rivers ta ce an sace tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta kasar, Okey Wali.

A ranar Asabar da daddare ne wasu 'yan bidiga suka sace shi a Fatakwal, babban birnin jihar.

'Yan bindigar sun tare motarsa ne a cikin birnin, suka yi awon gaba da shi.

'Yan sanda sunce suna can suna kokarin ceto shi.

Sun ce sun riga sun gano inda 'yan bindigar suka yasar da motarsa.

Kakakin rundunar Ahmed Mohammed ya gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa suna kokarin su ga sun ceto shi "cikin koshin lafiyarsa".

Karin bayani