Majalisar Birtania ta amince da Palasdinu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ginin majalisar dokokin Birtania

'Yan majalisar dokokin Birtania sun kada kuri'ar amincewa da gagarumin rinjaye da kasancewar kasar Palasdinu.

Sai dai sakamakon kuri'ar ba zai zama wajibi ba gwamnati mai ci yanzu ko wata a gaba ta aiwatar da shi.

Kuri'ar ta samu amincewa da rinjaye sosai ko da ike kasa da rabin yawan 'yan majalisar ne suka kada kuri'ar saboda ministocin gwamnati sun kaurace wa zaman.

Wani dan majalisa na bangaren 'yan adawa na jam'iyyar Labour shi ne ya gabatar da bukatar yin kuri'ar, yana mai cewa abu ne mai matukar muhimmanci 'yan majalisar su yi muhawara akan batun domin nuna matsayin al'umma game da rikicin Gabas ta tsakiya.

Duk da yadda sakamakon ya kasance ganin yadda 'yan majalisar na bangaren gwamnati da ke rike da mukaman ministoci suka kaurace wa zaman, da alamu abu ne mai wuya matsayi da manufar Birtania kan amincewa da kasar Palasdinawan su sauya a nan kusa.

Dan majalisar Birtaniyan na bangaren 'yan adawa na jamiyyar Labour Jeremy Corbyn ya yi maraba da sakamakon.

Kuri'ar ta Birtaniya ta biyo bayan kudurin da sabuwar gwamnatin Sweden ta masu ra'ayin kawo sauyi ta ayyana ne na amincewa da kasar Palasdinu.

Matakin da gwamnatin Isra'ila ta nuna bacin ranta akai, Amurka kuma ta yi alla-wadai da shi da cewa lokacinsa bai kai ba.

Karin bayani