Ebola: Ma'aikatan lafiya na yajin aiki a Liberia

Image caption Akalla ma'akatan lafiya casa'in da biyar ne suka mutu zuwa yanzu sakamakon cutar ta Ebola a Liberiya.

Wani yajin aikin kasa gaba daya da ma'aikatan lafiya suka shiga a kasar Liberia mai fama da cutar Ebola, bai yi tasiri ba.

Ma'aikatan lafiyar na neman karin alawus ne da ya shafi hatsarin da ke tattare da jinyar masu cutar Ebola, da karin kayan kare-kai, da kuma Inshora.

Gwamnatin kasar ta ce yadda annobar ke ci gaba da yaduwa ta sa ba za ta iya biyan ma'aikata kudin da ta amince da su a baya ba.

Kungiyar ma'aikatan lafiyar ta bukaci a yi wa 'ya'yanta karin kudaden yiwuwar fada wa hatsari da ake biyansu lokacin da suke yi wa masu cutar Ebola magani.

Ta kuma bukaci a sama wa 'ya'yanta isassun kayyakin kariya daga cutar Ebola da kuma inshora.

Gwamnatin Liberiya ta dage cewa, ba za ta iya yin karin albashi ga ma'akatan jinyar ba ta kuma bukaci kada su yi watsi da marasa lafiya.