Masu kamuwa da Ebola na ninkawa - UN

Hakkin mallakar hoto v
Image caption Majalisar Dinkin Duniya ta ce jami'an lafiya na kokarin yi wa cutar ebola rubdugu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen da ke kamuwa da cutar ebola a yammacin Africa na yin kamari, inda adadin ke ninkiwa a duk wata.

Fiye da mutane 4000 ne dai suka mutu sakamakon kamuwa da cutar ya zuwa yanzu.

Majalisar ta Dinkin Duniya ta ce tana sake sabon shirin tunkarar cutar ta ebola mai saurin kisa.

Wani babban jami'in Majalisar, Tony Banbury, ya shaida wa manema labarai a Accra, babban birnin kasar Ghana cewa jami'an lafiya daga sassa daban-daban na duniya na yin tururuwa zuwa kasashen da ke fama da cutar domin ba da agaji kan yadda za a dakile ta.

Karin bayani