'Sojin Nigeria sun saki mutane 111'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan uwan mutanen da aka kashe sun koka

Daya daga cikin mutanen da ya tsallake rijiya da baya lokacin da jami'an tsaro suka kai samame a unguwar Durimi, sannan suka kashe mutane biyar ya shaida wa BBC cewa an saki mutane 111 a cikin mutanen da aka kama.

Mutumin, wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya ce yanzu saura mutane talatin ake tsare da su

A samamen da sojin suka kai dai sun kuma raunata mutane da dama.

An kai samamen ne a wani sansanin da 'yan gudun hijarar da suka zo Abuja daga Borno suke samun mafaka.

'Yan uwan mutane da aka kashe sun shaida wa BBC cewa sun yi matukar mamaki da kisan mutane, kasancewa sun zo babban birnin ne domin gudun hijara amma aka zarge su da zama 'yan kungiyar Boko haram.

Wata kungiyar kare hakkin dan adam mai suna Civil Right Congress dai ta ce za ta bi kadin kisan da aka yi wa mutanen.

Karin bayani