Nigeria ta bayyana kwarin gwiwa kan dakarun hadaka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana sa ran taron Abuja zai samar da wani ingantaccen tsari don aiwatar da shawarwarin da taron Niamey ya cimma cikin nasara.

Shugaban Nigeria Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana kwarin gwiwar cewa kawancen kasar da makwabtanta zai taimaka wajen dakile ayyukan tada-kayar-baya da na bata-gari a kan iyakokinsu.

Da yake maraba da ministocin tsaro da na harkokin wajen Chadi, Nijar, Kamaru da jamhuriyar Benin a Abuja, shugaban Nigeria, ya ce bunkasa sintirin hadin gwiwa da aikace-aikacen sojoji da musayar bayanai tsakanin kasar da makwabtanta kamar yadda taron Niamey na makon jiya ya cimma zai murkushe ayyukan tada-kayar-baya.

Ministocin kasashen biyar na taro ne a Abuja don ganin yadda za su yi aiki da takwarorinsu na Nigeria kan wani jadawalin doka na ayyukan sojoji a kan iyakokin kasashe wanda taron Niamey ya amince da shi.

Wata sanarwa da Mai bai wa Goodluck Jonathan shawara kan harkokin yada labarai, Reuben Abati ya fitar ta ce shugaban ya yi imani cewa hadin gwiwar ya zama wajibi don samun nasarar yaki da ta'addanci.

Sanarwar bayan taron Niamey ta ce ya zuwa ranar 20 ga watan Nuwamba, za a samar da cibiyar wata rundunar dakarun hadin gwiwa da wani babban hafsan soja zai jagoranta.

Shugabannin sun kuma cimma shawarar cewa ya zuwa ranar 1 ga watan Nuwamba za a tura dakaru kamar yadda kowaccensu ta yi alkawari don kafa rundunar dakarun hadin gwiwa a cikin iyakokin kasashensu.

Ministocin sun hadar da na harkokin wajen Nijar, Mallam Bazoun Mohammed, da takwaransa na tsaro Mahamadou Karidjo, sai ministan wajen Kamaru Pierre Moukoko Mbonjo, da takwaransa na tsaron kasar, Mr. Edgar Alain Debe Ngo'o sai ministan tsaron Chadi, Mr. Benaindo Tatola da na harkokin wajen kasar, Muossa Faki Mahamat, da ministan tsaron Benin Mr. Robert Yarou, da takwaransa na harkokin waje Mr. Nassirou Bako Arifari.