An nemi yanke wa Pistorius hukuncin hidima

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Joel Maringa ya ce Pistorius zai iya hidimtawa al'umma tsawon sa'o'i goma sha shida a kowacce wata.

Daya daga cikin shaidun da ke kare dan tseren Afirka ta kudu da ake tuhuma da kashe budurwarsa, Dr Lore Hatzenberg ta ce rayuwa ce ta daburce masa.

Ta ce kamata ya yi a yi wa Oscar Psitorius, hukuncin yi wa al'umma hidima maimakon dauri a gidan yari.

Haka zalika, wani shaida daga hukumar gyara halayyar mutane ta Afrika ta Kudu da ya bayyana a madadin masu kare Pistorious, ya ba da shawarar a yanke wa Oscar pistorious hukuncin daurin shekaru uku amma ta hanyar talala da sanya masa ido a gida, saboda harbe Reeva Steenkamp.

Mr Joel Maringa na hukumar ya shaida wa kotun da ke zamanta a Pretoria cewa, ba kawai suna son a sanya Pistorious gwale-gwale ba ne, suna so ne a gyara masa hali ta yadda zai amfani al'umma nan gaba.