Samsung zai kara saurin Wi-Fi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Samsung ya ce nan da 'yan shekaru fasahar za ta shafi rayuwar mutane ta yau da kullum

Kamfanin Samsung ya ce ya gano hanyar da zai kara saurin tura bayanai da sauran abubuwa(data) ta wi-fi linki biyar akan yadda yake a yanzu.

Ya ce kwararrun ma'aikatansa sun shawo kan wasu manyan matsaloli biyu da suke hana tura bayanai(data) a kasa da tafiyar 4.6Gbps.

Idan wannan fasaha ta tabbata, hakan na nufin za a iya tura bayani ko wani abu mai nauyin 1GB cikin kasa da dakika uku.

Sai dai kuma wasu kawararru na ganin za a dauki lokaci kafin a sanya fasahar a wayoyi da sauran na'urori.

A wata sanarwa da kamfanin na Samsung ya fitar, ya ce, ma'aikatansa na aiki akan yadda wi-fi zai rika aiki akan tsarin 60GHz.

Hakkin mallakar hoto RIA Novosti

Wi-Fi da ake da shi a yanzu yana aiki ne akan tsarin 2.4 da 5GHz kuma wasu sukan iya tura 1Gb a cikin dakika daya.

Samsung din ya kuma ce ya yi nasarar rage yawan matsalar da bayanan da ake turawa ke fuskanta idan wayoyi ko na'urori da dama na hade akan wi-fi daya.

Na'urorin da za su fara amfani da fasahar tura bayanan cikin sauri ta 60GHz ana sa ran za su shigo kasuwa a 2015.

Kamfanin ya ce yana shirin sanya fasahar a talabijin da kayan aikin asibiti da wayoyin salula.