ISIS: Turkiyya ta ba da hadin kai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Susan Rice ta yaba da sauya shawarar da Turkiyya ta yi a yaki da ISIS

Mai bai wa shugaban Amurka shawara a kan tsaron kasa Susan Rice ta ce a yanzu Turkiyya ta amince sojojin da kawancen da Amurka ke jagoranta su yi amfani da filayen jiragen samanta na soji wajen kai hare-hare ga mayakan kungiyar masu da'awar kafa daular musulunci.

Susan Rice ta yi wadannan kalaman ne yayin da ake cigaba da tattaunawa tsakanin jami'an na Amurka da Turkiyya a kan rawar da Turkiyyar za ta taka a yaki da kungiyar ta masu fafutukar kafa daular ta Musulunci.

Da take magana a wata tashar talabijin ta Amurka Rice ta yi maraba da da abin da ta kira sabon kudurin Turkiyya na yaki da kungiyar masu rajin jihadin.

Sakamakon wannan mataki Amurka da kawayenta za su samu damar horad da mayakan 'yan tawayen Syria masu matsakaicin ra'ayi a yankin Turkiyya.

Amincewar Turkiyyan za ta sassauto da damuwar da Amurka ta yi kan kin da Turkiyyan ta yi da farko na mara baya yadda ya kamata a yaki da 'yan ISIS.