Boko Haram: Amfani da karfi ya rura wuta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan kungiyar Boko Haram na amfani da manyan makamai a yakin da suke yi

Cibiyar Chatham House da ke Birtaniya ta ce amfani da karfin soji shi ne ya kara janyo tabarbarewar rikicin Boko Haram a Najeriya maimakon magance shi.

A rahoton kungiyar mai gudanar da bincike da shirya mahawara kan harkokin cigaban kasashe, ta ce, matakin sojin ya harzuka 'yan kungiyar ne kawai.

Farfesa Marc-Anthoine na wata jami'a a Paris wanda ya gudanar da binciken, ya ce wannan mataki shi ya sa 'yan Boko Haram din suke kai hari kan kowa da kowa, sabanin yadda suke da farko.

Rahoton ya ce akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta bullo da dabaru masu sassauci na dakile rikicin.

Amma kuma ya zargi gwamnatin kasar da rashin rungumar tattaunawa da 'yan kungiyar tsakani da Allah, domin kawo karshen matsalar.

Karin bayani