An samu 'yar Nigeria da laifin safarar mata

Wata kotu a Burtaniya
Image caption Duka mutanen biyu dai an same mu da laifukan da ake tuhumarsu da aikatawa.

Wata kotu a Cardiff Crown da ke Burtaniya ta samu wata 'yar Najeriya da laifin safarar wasu mata 2 zuwa kasar domin su shiga sana'ar karuwanci.

Matar mai suna Lizzy Idahosa ta yi amfani da asirin Juju domin matan su ji tsoron kin amincewa da duk wani abu da ta umarci su yi.

Mutum na biyu da ake tuhuma mai suna Jackson Omoruyi shi ma an same shi da laifin safarar kudaden haram.