Watanni 6 bayan sace 'yan matan Chibok

Hakkin mallakar hoto AP

A Talatar nan ne 'yan matan Sakandaren Chibok fiye da 200 da Boko Haram ta sace a jihar Bornon Nigeria suka cika watanni shida a hannun kungiyar.

'Yan kungiyar Boko Haram ne suka far wa makarantar 'yan matan da ke garin Chibok a ranar 14 ga watan Afrilu, inda suka zuba su a motoci suka tsere.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu daga cikin iyayen 'yan matan har yanzu na fatan cewa hukumomi za su ceto 'ya'yan nasu

Kalilan daga cikin 'yan matan sun yi nasarar kubuta a kan hanyar kai su dajin Sambisa, inda ake jin 'yan kungiyar Boko Haram sun tsare su tun da farko, yayin da wasu fiye da 200 ke ci gaba da kasancewa a hannun kungiyar har yanzu.

Gangamin ceto 'yan matan Chibok mai taken Bring Back Our Girls ya yi suna a fadin duniya, inda fitattun mutane da shugabanni suka dora a kan kiraye-kirayen neman a saki daliban.

A baya dai, rundunar sojin Nigeria ta yi ikirarin cewa ta san inda ake tsare da 'yan matan, sai dai ba ta son yin amfani da karfi wajen kubutar da su don kauce wa asarar rayuka.

Haka zalika, gwamnatin Nigeria da takwarorinta na kasashen duniya da sauran Hukumomi sun sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen ganin an sako 'yan matan amma dai har yanzu shiru kake ji.

Hakkin mallakar hoto AP

A watan Yuli ne, Matashiyar nan 'yar Pakistan da ta tsallake rijiya da baya a lokacin da 'yan Taliban suka harbe ta a ka, Malala Yousafzai ta kai ziyara Nigeria don kara matsa lamba a yunkurin ganoinan sako 'yan matan Chibok da aka sace.

A baya-bayan nan kuma, an gano wata yarinya da aka yasar bayan sace ta tsawon watanni, ko da yake, daga bisani rahotanni sun ce ba ta cikin 'yan matan na Chibok.

Hakkin mallakar hoto AFP

Mutane da dama na tambayar shin ina 'yan matan Chibok suke a halin yanzu, kuma mece ce makomarsu?