Malala ta daga murya kan 'Yan matan Chibok

Image caption A Talatar nan ne 'yan matan Chibok suka cika watanni shida a hannun kungiyar Boko Haram

Matashiyar nan mai fafutuka 'yar Pakistan, Malala Yousufzai, ta yi kira ga gwamnatin Nigeria ta ribanya kokari don ganin kungiyar Boko Haram ta saki 'yan matan Chibok fiye da 200 da ta sace.

Malala Yousufzai wadda ta zama mutum mafi karancin shekaru da ya taba lashe kyautar Nobel kan zaman lafiya ta ce "watanni shida bayan sace 'yan matan sakandare 273 a Nigeria jazaman ne mu sake daga murya fiye da a kowanne lokaci"

A shafinta na intanet ta wallafa bukatar ganin an sako 'yan mata fiye da 200 da ake tsare da su don su koma wajen iyayensu, su kuma samu ilmi ingantacce cikin aminci.

Ta ce "na roki gwamnatin Nigeria da sauran kasashen duniya su kara ribanya kokari don kawo karshen wannan lamari cikin hanzari da lumana."