'Yan sanda sun hana masu zanga-zanga shiga Aso Rock

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sandan sun yi dogon layi a kan hanya inda suka hana masu zanga-zangar wucewa

'Yan sandan Nigeria sun tare masu zanga-zangar neman a saki 'yan matan Chibok fiye da 200 daga yin maci zuwa fadar shugaban kasa watanni shida bayan sace su.

'Yan sanda mata ne cikin kayan aikin kwantar da tarzoma suka yi shinge don hana 'ya'yan kungiyar Bring Back Our Girls wucewa.

An kiyasta cewa jami'an tsaro da aka tura wajen sun ninka adadin masu zanga-zangar da ke rera taken "A dawo mana da 'ya'yanmu yanzu kuma da ransu" har sau goma.

Masu fafutukar sun shirya zanga-zangar ne zuwa fadar shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan don kara matsa lamba wajen ganin an sako 'yan matan.

Masu fafutukar na zargi gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan da gazawa wajen ceto 'yan makarantar duk da alkawuran da ta dauka na yin hakan.

Daya daga cikin jagororin kungiyar BringBackOurGirl da ke kokarin ganin an sako 'yan matan, Hadiza Bala Usman ta shaida wa BBC cewa gwamnati ta ki bai wa jami'an tsaro kayan aikin da suka dace don fatattakar 'yan Boko Haram, su kuma ceto 'yan matan.