Cutar Ebola: Ko an kawar da cutar a Nijeriya?

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Har yanzu cutar Ebola na ci gaba da hallaka mutane a wasu kasashen Afirka ta yamma, yayin da kuma cutar ta shiga Turai da Amurka

A ranar litinin 20 ga wannan wata ne Nigeria za ta san matsayinta game da kasancewa ko akasin kasancewar kwayoyin cutar Ebola a kasar.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta debar wa Nigeria kwanaki 42 na tilas, kafin ayyana ta a matsayin kasar da babu wani mai dauke da cutar Ebola.

Hukumar ta tabbatar cewa ta kammala aikin bibiyar mutanen da aka san sun yi hulda da wani mutum da ya kamu da Ebola a Legas, yayin da a fatakwal aikin ya kai kaso 98 cikin 100.

Rahotanni sun ce duk mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar Ebola a Nigeria suna da alaka da dan Liberiyar nan, Patrcik Sawyer da ya je kasar da Ebola ranar 20 ga watan Yuli.

Haka zalika, ana sa ran Hukumar za ta ayyana kawo karshen cutar Ebola a kasar Senegal ranar Juma'a 17 ga wannan wata.

Shelar Hukumar lafiya ta duniya da ake sa rai a kan kawo karshen barkewar Ebola a wadannan kasashe biyu, abin maraba ne ga al'ummar duniya kan wannan annoba da ta zame wa wasu kasashen Afirka ta yamma alakakai