Facebook ya ba da $5m don yaki da Ebola

Mark Zuckerberg Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Kudin dai za a yi amfani da su ne don yakar yaduwar cutar Ebola.

Mutumin da ya kirkiro shafin sada zumunta na Facebook Mark Zuckerberg ya sanar da cewa ya ba da tallafin dala miliyan 5 don yaki da cutar Ebola.

Mr. Zuckerberg ya ce cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Amurka ce za ta yi amfani da kudin.

Ya ce Facebook ya ba da tallafin ne don ganin cewa cutar ba ta zama wata babbar annoba da za ta dade ana fama da ita a duniya ba.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya yaba da wannan babbar gudummawa da Facebook ya bayar.