Mr Ban ya nuna jimami kan lalata Gaza

Mr Ban Ki-Moon Hakkin mallakar hoto
Image caption Mr Ban ya nuna jimami da barnar da aka yi a yakin da aka kwashe makwanni 7 na yi tsakanin Plasdinu da Israela

Sakatare janal na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon, ya bayyana barnar da aka yi a Zirin Gaza sanadiyyar yakin da aka gwabza tsakanin Palasdinu da Israela da abinda ya shallake hankali.

A wata takaitacciyar ziyara da ya kai, Mr Ban yace barnar da aka yi a wannan karo ta rubanya wadda ta faru a yakin da bangarorin biyu suka yi da juna shekaru 5 da suka gabata.

Ziyarar tasa na zuwa ne bayan da aka yi taron neman tallafi a kasar Masar domin sake gina Gaza, wanda ake bukatar fiye da dala bliyan 5 domin wannan aiki.