An samu maza 5 da laifin fyade a India

Masu zanga-zanga da kin amincewa da yi wa mata fyade a India Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mazan sun yi wa matar fyade a cikin karamar motar daukar kaya.

An samu wasu maza 5 da laifin yi wa wata ma'aikaciyar gidan waya a birnin Delhi fyade, a wata shari'a da ta sanya aka kara daukar matakan kare ma'aikata mata.

An dai samu mazan da laifin yi wa matar fyade a cikin karamar motar daukar kaya da sanyin safiya, a lokacin da take kan hanyar komawa gida bayan ta yi aikin kwana.

Saboda wannan mummunan abu da ya samu ma'aikaciyar, gidan waya da sauran ma'aikatu sun bullo da wani tsari da zai kare mata ma'aikata mata.

Ciki har da samar da motar da za ta rin ka sauke su a kofar gidajensu bayan sun tashi dagawajen aiki.