An saci bayanai a kantin Kmart.

Makeken Kantin Kmart Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Makeken Kantin Kmart

Makeken Kantin nan Kmart ya bayar da rahoton cewa barayi sun tura kwayoyin cutar Komfuta a shafinsa na cajin kudade na kantunansa dubu da dari 2.

A cikin wata sanarwa, Makeken Kantin na Kmart ya ce a ranar 9 ga watan Oktoba ne aka gano cewar barayin sun yi kutsen, amma tun farkon watan Satumba shafukkan na cajin kudade na masu sayayyar suka harbu da kwayoyin cutar.

Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewar barayin ta Internet sun saci bayanai da lambobi na katunan biyan kudade na masu sayayya a kantunan.

Kawo yanzu dai ba a tantance ko mutane nawa aka saci bayanan katunan na su ba, ko kuma adadin mutanen da abin ya shafa.

A wata sanarwa, Makeken kantin na Kmart ya ce, ba a saci bayanan sirri na mutane ba ko lambobin sirri nakatunan da adireshin email a satar da aka yi ta lambobin kantunan masu sayayya a kantin.

A yanzu dai an cire kwayoyin cutar da aka tura shafukkan na cajin kudi na komputar kamfanin, to amma kamfanin yana cigaba da bincike don gano cikakkiyar illar da satar za ta haifar.

Kamfanin ya kara da cewa, babu wata shaida da ta nuna cewar lambobin katunan da aka sata, an yi amfani da su ne don yin wasu katunan na jabu wadanda za a rinka amfani da su wajen sayayya a wasu wurare.

Duk da wannan, kantin na Kmart ya ce zai bayar da kariya ta cin bashi ga masu katunan da aka saci lambobinsu don tabbatar da cewa duk wata zamba da aka yi, ba ta shafe su ba.

Hukumar leken asiri ta Amurka wadda ke jan ragama a binciken zambar kudade, tana gudanar da bincike kan lamarin.

Karin bayani