Masu kutse na Rasha sun farma NATO

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun lokacin da aka fara rikicin Ukraine ake ganin an samu karuwar satar bayanai ta intanet

Masu kutse ta intanet na Rasha sun yi satar shiga kwamfutocin kungiyar tsaro ta Nato da na wasu gwamnatocin yammacin duniya ta wata hanyar Microsoft Windows.

Rahotan da ya bayyana haka ya ce, ta wannan hanya ce aka yi satar shiga kwamfutocin Ukraine da Poland.

Kamfanin harkokin tsaro ta intanet iSight Partners, ya ce bai san wadanna bayanai masu kutsen suka duba ba, amma ya ce yana ganin suna neman bayanai ne akan rikicin Ukraine.

Kamfanin Microsoft ya ce zai toshe hanyar da masu satar bayanan suka yi amfani da ita wajen shiga kwamfutocin.

Wani mai magana da yawun kamfanin ya ce, Microsoft zai samar da manhajar da za ta sabunta dukkanin kwamfutocin da suke da wannan rauni ko matsala kai tsaye da za su gyaru da kansu.

Hakkin mallakar hoto hackers
Image caption Wani mai satar bayanai ta intanet

Daga bisani mai magana da yawun kungiyar tsaron ta Nato ya fitar da wata sanarwa dangane da lamarin satar bayanai ta kwamfutocin nata.

Ya ce, ''Nato na duba shedar zargin kutsen da rahoton ke cewa an yi wa kwamfutocinta''.

Sauran kafofin da ake ganin masu kutsen sun saci bayanai a kansu, sun hada da fannin makamashi da sadarwa da kamfanonin tsaro da kuma wani masani kan dangantaka tsakanin Rasha da Ukraine.

Ko da ike kamfanin da ya gano wannan kutse, bai iya tabbatar da cewa ko masu satar bayanan suna da alaka da gwamnatin Rasha ba, wani masani na ganin da alamun goyon bayan gwamnati saboda masu kutsen bayanai suke nema ba satar kudi ba.