Ranar wanke hannu ta duniya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Majalisar dinkin duniya na jaddada muhimmancin wanke hannu domin kaucewa kamuwa da cutuka

Yau ce ranar da majalisar dinkin duniya ta ware domin jaddada muhimmancin wanke hannu da sabulu domin tsafta.

Majalisar ta ware kowacce rana ta 15 ga watan Oktoba domin nuna muhimmancin tsaftar hannu don magance matsalar kamuwa da cututtuka da ake dauka ta hannu.

Bullar cutar Ebola ta sa mutane da dama a wurare irinsu Lagos, kara daukar matakan tsaftace hannuwansu.

Wasu kan kauracewa yawan musabaha, yayin da wasu kuma kan yi amfani da sinadarin tsaftace hannu na 'sanitizer'.

Sama da mutane miliyan 200 a kasashe 100 ke mutunta ranar wanke hannun ta duniya kamar yadda majalisar dinkin duniya ta ce.