'Yan tawaye sun karbe garin Hodeida

'Yan tawayen kabilar Houthi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mabiya darikar shi'a na kabilar Houthi sun dade su na tada kayar baya a kasar ta Yemen.

Rahotanni daga kasar Yemen na cewa 'yan tawaye mabiya darikar Shi'a sun kwace garin Hodeida mai muhimmanci da ke gabar teku, da kuma filin tashi da saukar jiragen saman garin hadi da gabar tekun.

'Yan tawayen na kabilar Houthi wadanda a watan da ya gabata suka kwace iko da babban birnin kasar Sanaa, sun kutsa garin na Hodeida tare da kai hare-hare ba kakkautawa.

A ranar litinin ne dai 'yan kabilar Houthi su kai marhabin da nadin Khalid Bahah a matsayin sabon Prime Ministan kasar Yemen.

Bayan da suka tilastawa tsohon Prime Ministan yin murabus a watan ya gabata.

'Yan kabilar Houthi na ta tada kayar baya lokaci zuwa lokaci tun daga shekarar 2004, don samun karin iko a yankin arewacin Saada da ke da muhimmanci.