Faransa ta hana yi wa barasa shan mankas

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption A baya-bayan ne ma Ma'aikatar bunkasa al'adun kasar ta bullo da wani yunkurin wayar da kai game da shan barasa a yi mankas

Hukumomi a Faransa sun sanar da cewa sun bullo da matakan dakile shan barasa a bugu a fadin kasar.

Hukumomi sun ce za su maida halayyar ingiza kananan yara su sha barasa fiye da kima a matsayin babban laifi.

Mutanen da aka samu da aikata wannan laifi za su fuskanci daurin shekara guda a gidan yari da kuma tarar dala 19,000.

Ma'aikatar lafiyar Faransa ma tana son haramta kayayyakin da suka hadar da riguna da wayoyin salula da ke kwarzanta shan barasa.

Ana ganin shan barasa a yi marisa a matsayin wata matsala da ke karuwa a tsakanin matasan Faransa, fiye da rabin matasa 'yan shekaru 17 sun ce sukan sha barasa su yi tatul akalla sau daya a wata.