Buhari ya yi shelar takarar shugaban kasa

Janar Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Janar Muhammadu Buhari

Tsohon Shugaban mulkin Sojin Nijeriya Janar Muhammadu Buhari ya yi shelar tsayawa takarar Shugabancin Nigeria a inuwar jam'iyyar adawa ta APC a zabukan shekarar 2015.

Janar Buhari ya bayyana aniyar tsayawa takarar shugabancin Najeriyar ne, a wani gangami da aka yi a larabar nan a filin taro na Eagle Square da ke Abuja babban birnin Nijeriya.

Tuni dai, tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar shi ma ya bayyana aniyar sa ta tsayawa takarar karkashin jam'iyyar ta APCn, yayinda ake ganin wasu 'yan takarar irinsu gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso da tsohon mawallafin jaridar Leadership Sam Ndah Isiah su ma za su biyo baya.

Janar Buharin ya ce, ya fito ne saboda jama'a sun nemi ya sake tsayawa takara, sabanin kalamansa a can baya, na cewar ba zai sake yin takara ba.

Janar Muhammadu Buhari ya fara jawabinsa ne da jajantawa al'ummar Nigeria da ke fama cikin fatara da rashin tsaro sakamakon ayyukan 'yan tada-kayar-baya da wasu mutane da ya ce marasa tsoron Allah ke aikatawa da sunan Boko Haram.

Ya kuma yaba wa jami'an tsaro da 'yan sanda a kokarinsu na dawo da zaman lafiya a Nigeria, ya kuma bukaci su ci gaba har sai sun cim ma nasara.

Muhammadu Buhari ya ce "Cikin kaskantar da kai, nake gabatar da kaina ga dukkan 'yan Nigeria da kuma ubangijina Allah don neman a zabe ni a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC".

Karin bayani