Ranar tuka abin hawa ba ham a jihar Legas

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lagos, shi ne gari mafi yawan ababen hawa a Nigeria da ke janyo yawan hayaniyar gari

Gwamnatin jihar Legas a Nigeria ta bukaci direbobi kada su busa ham din motocinsu tsawon wannan rana a yunkurin rage hayaniyar gari.

Manufar bullo da ranar da ba a busa ham ita ce kyautata da'a da ladubban direbobi a kan tituna da kuma rage gurbata muhalli.

Yawan bushe-bushen ham din motoci wata siffa ce ta rayuwa a birnin Legas, yayin da masu ababen hawa ke kokarin samun hanya a cikin cunkoso.

Sai dai rahotanni sun ce direbobi da dama ne suka ci gaba da busa ham din motocinsu a wannan rana da ake sa ran kowanne abin hawa zai tafi ba tare da hayaniya ba.