Bincike: Matasa da dama sun shaku da internet

Image caption Binciken ya nemi jin ta bakin jama'a ko suna nuna rashin kulawa ga 'yan uwa saboda internet

Wani bincike da aka gudanar ya yi nuni da cewa matasa da dama na fama da matsalar shakuwa da internet

Binciken wanda Digital Clarity ta gudanar akan matasa 1,300 ya gano cewa kashi 16% na matasa masu shekaru 18 zuwa 25 sun nuna alamun shakuwa da internet.

Kusan dukkanin wadannan kashi 16% din sun bayyana cewa suna shafe sama da sa'oi 15 a rana suna amfani da Internet.

Kawunan Kwararru ya rabu game da yadda matsalar take a zahiri

Binciken ya kalli wasu alamu guda biyar na yiwuwar fadawa irin wannan hali na shakuwa da Internet

Abubuwan sun hada da shafe sa'oi masu yawa a internet da jin haushi idan aka katse wa mutum lokacinsa na internet da mutum ya rinka jin cewa ya yi laifi saboda lokutan da yake dauka yana amfani da internet da killace kai daga 'yan uwa da abokai saboda internet.

Malissa Scott wani daliba ne a Middlesex, kuma ya yi imanin cewa yana fama da wannan matsala ta shakuwa da internet

Ya ce yasan wannan matsalar ta yi illa ga dangantakarsa da abokanansa da kuma sauran 'yan uwa.

Binciken da aka gudanar a baya ya nuna cewa wannan matsalar data hada da yin wasanni a internet da kallon shafukan batsa tana da dangantaka da shakuwa da shan miyagun kwayoyi.