Ana artabu da dakarun Janar Haftar a Libya

Janar Haftar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Janar Haftar

Dakarun dake goyon bayan tsohon Janar na kasar Libya Khalifa Haftar na ta hankoron sake kwace ikon gabashi birnin Benghazi daga mayakan Islama.

Shaidu sun ce an yi ta jin karar harbe harbe da fashewar abubuwa a gundumomi da dama.

Gwmanatin Libya ta ce tana goyon bayan Janar Haftar wanda aminin tsohon shugaban kasar ne marigayi Muammar Gaddafi.

Gwamnatin ta ce dakarun kasar Libyar na fafatawar tare da dakarunsa.

A cikin watan Mayu ne Janar Haftar ya kaddamar da yunkurin kwace ikon birnin Banghazin, amma mayakan Islamar suka samu galaba a kan sa.