Shari'ar sojojin Najeriya da ake zargi da tawaye

Hakkin mallakar hoto Reuters

A Najeriya, a yau ne wata kotun soja za ta ci gaba da sauraren karar da aka shigar akan wasu sojojin kasar su 59, bayan da aka zarge su da laifin yin tawaye a lokacin da aka basu umurnin su tunkari 'yan kungiyar Boko Haram a kauyen Delwa da ke Maiduguri.

Dukkanin sojojin da ake tuhuma dai sun musanta laifukan da ake masu .

Wannan shi ne karo na biyu da rundunar sojin kasar za ta gurfanar da sojoji gaban kotu bisa zargin aikata ba dai dai ba.

A baya wata kotu ta sami wasu sojoji da laifi kan boren da suka yi a Maiduguri, abin da ya ta yanke ma wasu daga cikinsu hukuncin kisa .